Wani Neman Jarumai . Морган Райс
SURA NA DAYA
“kan da yasa hulan sarauta baya samun sauki”
--William Shakespeare
A Littafin Henry IV, Shashi na biyu
SURA NA DAYA
Yaron ya tsaya a kan kololuwar karamar tudun kasar da take kasa kasa a masarautar yamma na zoben, ya kalli arewa, yana kallon farkon tasowan rana. A iya nisan kallonsa, yana ganin koren shinfidaddun tudu, wayanda suna sauka su haura kaman tozon rakumi a cikin wadansu kwari da ganiyan tudu. Hasken bullowan ranar farko mai launin ruwan lemu ya dan dade yana haskawa a kan rabar safe, yana sa su kyalli, yana ara wa hasken, majigin da yayi dede da yadda yaron yake ji a ran sa. Yaron bai cika tashi da wuri haka ba kuma bai taba nisan kiwo daga gida haka ba – kuma bai taba haurawa tudun da tsawo haka ba – domin yasan yin hakan zai jawo fushin mahaifinsa. Amma a wanan ranar, bai damu ba. A wannan ranar, yayi biris da miliyoyin dokoki da ayyuka masu yi masa danniya na tsohon shekaru goma sha hudu. Hakan ya faru ne saboda wannan ranan na daban ne. Rana ne da ya kasance kaddararsa ta iso.
Yaron, Thorgrin na masarautar yammacin daular yan dangin McLeod na kudu – sananne ga duk wadanda yaso da suna Thor kawai – dan auta cikin yara maza hudu, mafi karacin soyuwa a wurin mahaifinsa, ya kwana idonsa biyu saboda begen wannan rana. Yayi ta juye-juye, da idanu cike da ruwa, yana jira, yana fatan farkon tasowan rana. Saboda rana kamar haka yakan faru ne sau daya a cikin shekaru da yawa, kuma in har ya bar zarafin ya kubuce masa, zai makale a wannan kauyen, yakuma dawwama a aikin kula da garkunan mahaifinsa har iya rayuwarsa. Wannan kuma ya zama tunanin da ba zai iya hakuri da shi ba.
Ranar shiga soja . Ya kasance rana daya ne rak da sojojin sarki ke zaga wa duka dauloli suna zaban masu son shiga rundunan sarki. Tun da yake raye, Thor baya mafarkin komai face wannan. A wurin shi, ma’ anar rayuwa abu daya ne rak: shiga silver, zababbun hafsosin rundunar sarki, sanye da kayan adon yaki mafi kyau da kuma tattatun makamai a ko ina a cikin duka masarautai biyun. Kuma ba a shiga cikin silver sai mutum ya shiga babbar runduna, rundunonin masu koyan aikin tsaro da shekarun su ke sakanin goma sha hudu da goma sha tara. Kuma idon mutum bai kasance dan fittatun mutane ba, ko wani sanannen jarumi ba, to babu wata hanyar shiga babbar runduna.
Ranar shiga soja ne kawai ta sha banban, wannan abin ba safai ba, da ya ke faruwa a kowani shekara da rundunonin sarki ke raguwa kuma hafsosin sarki ke zaga kasan suna neman sabbobin dauka. Kowa ya san kalilan a ke daukawa a cikin yaku bayi – kuma musamman an san kadan ne daga ciki za su samu shiga babban runduna.
Thor ya karanci yanayin wuri sosai, yana dubawa ko zai ga wata alamar motsi. Yan silver, ya sani, ya zama dole su biyo nan, hanya makadaiciya zuwa kauyen sa, kuma yaso ya zama wanda zai fara ganin su. Garken tumakin sa na ta nuna rashin yarda a kewaye da shi, sun tada kukan haushi da murya daya kuma suna nuna su fa ya mayar dasu gangarar tudu, inda mafi kyawun ciyayi suke. Yayi kokarin ya toshe ihunsu, da kuma warinsu. Sai ya zama masa dole ya tara hankalinsa a guri guda.
Abinda yasa ya iya juran duka wannan, shekarun da yayi yana kiwo, yayi yana bauta wa mahaifinsa, yayi yana bauta wa yayunsa, yayi yana mai samun mafi karancin kulawa kuma mafi aikatuwa, shine zaton cewa watan watarana shi zai bar wannan wurin. Wata rana, idon yan silver sukazo, shi zai bawa duk wadanda suka raina masa mamaki da zabansa da za a yi. Farat daya shi zai dale amalankensu yayi bankwana da duk wannan damuwowin.
Mahaifin Thor, a kan huja, bai taba daukan shi da muhimmanci a matsayin dan takaran shiga rundunan tsaro ba – musamman ma, bai taba daukan shi a matsayin dan takaran komai ba. A madaddin haka, ya bada soyyayarsa da kulawa gabadaya wa yayun Thor su uku. Babban cikinsu dan shekaru goma sha tara ne kuma shauran sun bi juna da shekaru dadaya, wanda yasa Thor yazama kanin kowanne a cikin su da akalla shekaru uku masu kyau. Wata kila domin shekarunsu na kurkusa da juna kokuma watakila domin su sun yi kama da juna amma ba kama da Thor ba, su ukun a manne da juna suke a kowani lokaci, batare da sun nuna wani alaman sun san da rayuwar Thor ba.
Abinda yafi munima shine duk sun fishi tsayi da fadi dakuma karfi, shikuma Thor, duk da ya san shi ba gajere bane, Thor yaji cewa shi karami ne in an kwatanta dasu, yana raina ginannu kafafuwansa in ya kwatanta da nasu masu kama da manyan bishiyoyin gamji. Mahaifinsa bai dauki ko mataki saboda magance wannan ba – Kaman ma yana jin dadin haka ne – ya bar Thor ya dinga kiwon tumaki da wasa makamai alhalin yan’uwansa sunanan suna koyon yaki. Abinda ba a fada amma da kowa ya sani shine cewa, Thor zai karasa sauran rayunsa a dan kallo ne, zai tilasstu da kallon yan’uwansa suna yin abubuwan al’ajabi. Da mahaifinsa da yan’uwansa za su samu yadda suke so, da kaddarar sa zai zama, ya kasance a nan, a hadiye a cikin wannan kauyen, yana bawa iyalensa duk kular da suka nema a wurinsa.
Wani munin abin kuma shine cewa Thor ya fahimci cewa yan’uwansa, ta wata hanyan, suna jin shakkan shi, watakila ma sun tsane shi. Thor na iya ganin haka a kowane kalon su zuwa gare shi da yanayin